Kamfanin Dillancin Labaran Hauza: Canje-canjen shekarun baya-bayan nan sun nuna cewa tunanin da aka assasa tare da taken "Kiyam lillah" (Tashi tsaye saboda Allah) a cikin gwagwarmayar Imam Khumaini (Q), a yau ya tsallake iyakokin juyin juya hali na siyasa kuma ya zama wani babban tsarin wayewa. A mahangar Imam, gwagwarmaya ba kawai wani mataki ne na siyasa don sauya mulki ba; a'a, yunkuri ne na Ubangiji domin kafa adalci, kore mamaya, da farfado da asalin koyarwar Musulunci a fagen shugabanci. Wannan babban tushe ne ya sa Juyin Juya Halin Musulunci tun farkonsa bai takaita kansa ga wata iyaka ta kasa ko wani takamaiman lokaci na tarihi ba.
Makarantar tunani ta Imam Khumaini (Q) ta ginu ne akan hadakar hankali da koyarwar addini; wani tsari ne da cikinsa ba a raba siyasa da tarbiyya, kuma iko ba shi da ma'ana idan babu adalci. A cikin wannan tsari, kafa gwamnatin Musulunci ba shi ne babban burin karshe ba, a'a, hanya ce ta tabbatar da adalci da samar da sararin gina al'umma mai ci gaba da ta ginu akan dabi'un Ubangiji. A saboda haka ne, wannan makaranta ta iya gabatar da wani tsari na tsarin mulki na gari na addini, wanda a cikinsa sa hannun jama'a da shiryatarwa ta addini ke tafiya tare.
A gefe guda kuma, ka'idar "Ba ma yin zalunci, kuma ba ma karbar zalunci" tana matsayin daya daga cikin shika-shikan wannan tunani, wanda kuma shi ne ya tsara manufofin ketare na Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Juriya a gaban matsin lamba da takunkumai, goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya (Resistance), da kokarin kare 'yancin siyasa da na kimiyya na kasar, duka ana iya fassara su ne a cikin wannan tsari.
Masana da dama sun yi amincewa cewa dukkan wadannan canje-canje sun sanya Iran a gabar wani gagarumin sauyi na tarihi; wani mataki da zai iya zama shimfidar samun ci gaba na wayewar kai. Ketare wannan mataki tabbas an biya farashi kuma za a ci gaba da biya, amma abubuwan da suka faru a shekaru arba'in da suka gabata sun nuna cewa tsarin Juyin Juya Halin Musulunci ya nuna juriya mai karfi koda a gaban matsin lamba mafi tsanani.
A cikin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ta yi da Hujjatul Islam wal Muslimin Muhsin Mumini, memba a hukumar gudanarwa ta Cibiyar ilimi ta tarihin wannan zamani da Juyin Juya Halin Musulunci ta Hauza, kuma mai bincike akan Juyin Juya Halin Musulunci, mun tattauna wadannan batutuwa, kuma ga cikakken bayani kamar haka:
Yaya Makarantar Tunanin Imam Ruhullah da Shahidin Jagora Suka Sauya Ma'aunin Iko? / "Ba Ma Yin Zalunci, Kuma Ba Ma Karbar Zalunci"; Babban Ka'idar Jagoranci a Gwamnatin Juyin Juya Hali
Tambaya: A cikin watanni biyu ko uku da suka gabata, bayan farkon yakin danniya na Ramadan da kuma shahadar shugabanmu shahidi (Ayatullah Khamenei), mun yi tattaunawa da malamai da masana da dama. A cikin wadannan tattaunawa, an fi yin magana akan tushe da siffofin makarantar tunani ta Marigayi Imam (Khumaini) ta mahangar Shahidin Jagora; wani mutum da ya kwashe shekaru talatin da bakwai yana jan ragama da shiryar da al'umma, musamman ma a kowace shekara a ranar tunawa da rasuwar Imam a Haraminsa mai alfarma, inda yake bayyana muhimman abubuwa. Ina sha'awar jin mafi muhimman siffofi da rabe-rabe a wannan fage daga bakinku.
A yanzu kusan fiye da watanni uku ke nan tun bayan farkon yakin danniya, kuma a cikin wadannan watanni uku ko hudu da suka gabata abubuwa masu matukar muhimmanci sun faru. Daga yakin kwanaki goma sha biyu, har zuwa yanzu da aka kwashe fiye da shekara guda, mun shaida canje-canje masu yawa; da wuraren karfi da kuma wuraren rauni.
Idan muna son mu kalli wannan al'amari cikin adalci, lallai Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma rundunonin gwagwarmaya sun nuna bajinta ta kwarai; koda yake muna da wasu kasawa kuma akwai abubuwan da wasu daga cikinsu na fannin fasaha ne kuma ba sa cikin kwarewarmu, amma wadancan sassa da za mu iya fahimta ta mahangar ilimin bil'adama (Sciences Humanies) za su iya zama ma'aunar tattaunawarmu.
"Makarantar Tunanin Imam Khumaini (Q)"; Kalmar da Ta Yi Fice a Shekarun Baya-bayan Nan
Bari mu koma ga batun da kuka ambata; wato batun Makarantar Tunanin Imam Khumaini (Q). A kowace shekara a ranakun tunawa da rasuwar Imam, ana gabatar da wannan batu a tsakanin al'umma musamman a tsirarun makarantun addini (Hauzozi). Koda dai muna da bashin wannan batu ne daga Shugabanmu Shahidi, domin shi a kowace shekara a wajen taron tunawa da rasuwar Hazrat Imam, lokacin da yake jawabi, yana nuna muhimman abubuwa, kuma a shekarun baya-bayan nan ya kasance yana kawo bayanansa a karkashin kalmar sirri ta "Makarantar Tunanin Imam Khumaini (Q)".
Saboda haka, wannan kalma kadai tana dauke da ma'ana mai fadi sosai. Ba mu cika ganin wani mutum da Shugabanmu Shahidi ya yi amfani da kalmar "Makaranta" (Maktab) a kansa. Misali, sun ambaci "Makarantar Haj Qasim" (Solaimani); eh, watakila muna da wasu 'yan kalmomi kalilan na daban, amma ta fuskar amfani, nanatawa, da kuma cikar ma'ana, ba a cika samun misali kamar "Makarantar Tunanin Imam Khumaini (Q)" ba. Idan muka duba jawaban Shugabanmu Shahidi kuma muka binciko kalmar "Makarantar Tunanin Imam Khumaini (Q)" a cikin bayanansa, muna samun manyan abubuwa guda uku ko hudu na tushe.
Tushen Makarantar Tunanin Imam Khumaini (Q): "Kiyam Lillah" (Tashi Tsaye Saboda Allah)
Na farko shi ne, Shugabanmu Shahidi, Imam Khamenei, yana daukar tushen makarantar tunanin Imam Khumaini a matsayin "Kiyam lillah" (Tashi tsaye saboda Allah). Idan kuka duba littafin Sahifeh-ye Imam (Sahifar Imam), za ku ga cewa sako na farko na Imam Khumaini (Q) wanda nake kyautata zaton yana da alaka da shekarar 1323 (1944 Miladi) ne, shi ne sako na farko na rubutu da ya rage daga gare shi wanda ya zo mana, kuma yana cikin juzu'i na farko na littafin Sahifar. Ina ma tsammanin cewa asalin rubutun hannunsa ana ajiye shi ne a dakin karatu na garin Yazd.
A can ne Imam Khumaini ya gabatar da batun "Kiyam lillah". Salon yaren da aka yi amfani da shi a cikin wannan rubutu yana da zafi sosai, kuma Imam ya nuna bacin rai na kwarai a cikinsa. Wannan yana nuna cewa ya kasance cikin tsananin bacin rai da rashin amincewa da kungiyoyin da suka gabata a lokacin mulkin Reza Shah, da kuma kungiyoyin da suka shigo fagen addini da na boko suka kawo cikas, da kuma halin shiru da nuna halin ko-in-kula da aka fuskanta game da su.
Ra'ayinka